Acts 21

Zuwa Urushalima

1Bayan muka rabu da su da ƙyar, sai muka shiga jirgin ruwa, muka miƙe zuwa Kos. Washegari muka tafi Rods daga can kuma muka je Fatara. 2Sai muka sami wani jirgin ruwa da zai ƙetare zuwa Funisiya, sai muka shiga muka kama tafiya. 3Bayan muka hangi Saifurus muka wuce shi ta kudu, sai muka ci gaba zuwa Suriya. Muka sauka a Taya, inda jirgin ruwanmu zai sauke kayansa. 4Da muka sami almajirai a can, sai muka zauna da su kwana bakwai. Ta wurin Ruhu, suka yi ƙoƙari su hana Bulus wucewa zuwa Urushalima. 5Amma da lokacin tashinmu ya yi, sai muka tashi muka ci gaba da tafiyarmu. Dukan almajirai da matansu da ʼyaʼyansu suka raka mu har bayan birni, a can kuwa a bakin teku muka durƙusa muka yi adduʼa. 6Bayan mun yi bankwana da juna, sai muka shiga jirgin ruwa, su kuwa suka koma gida.

7Muka ci gaba da tafiyarmu daga Taya muka sauka a Tolemayis, inda muka gai da ʼyanʼuwa muka yi kwana ɗaya tare da su. 8Da muka tashi washegari, sai muka isa Kaisariya muka kuma sauka a gidan Filibus mai bishara, ɗaya daga cikin Bakwai ɗin nan. 9Yana kuwa da ʼyaʼya huɗu ʼyan mata waɗanda ba su yi aure ba, waɗanda suka yi annabci.

10Bayan muka yi ʼyan kwanaki da dama a can, sai wani annabin da ake kira Agabus ya gangaro daga Yahudiya. 11Da ya zo wurinmu, sai ya ɗauki ɗamarar Bulus, ya ɗaura hannuwansa da ƙafafunsa da ita saʼan nan ya ce, “Ruhu Mai Tsarki ya ce, ‘Haka Yahudawan Urushalima za su ɗaure mai wannan ɗamara su kuma ba da shi ga Alʼummai.’ ”

12Saʼad da muka ji haka, sai mu da mutanen da suke can muka roƙi Bulus kada ya je Urushalima. 13Sai Bulus ya amsa, ya ce, “Don me kuke kuka kuna kuma ɓata mini zuciya? A shirye nake ba ma a ɗaure ni kawai ba, amma har ma in mutu a Urushalima saboda sunan Ubangiji Yesu.” 14Da dai ya ƙi rarrasuwa, muka yi shiru, muka ce, “Bari Ubangiji yǎ yi nufinsa.”

15Bayan haka, sai muka shirya muka kuma haura zuwa Urushalima. 16Waɗansu almajirai daga Kaisariya suka raka mu suka kawo mu gidan Minason, inda za mu sauka. Shi mutumin Saifurus ne kuma ɗaya daga cikin almajirai na farko.

Isowar Bulus a Urushalima

17Saʼad da muka zo Urushalima, ʼyanʼuwa suka karɓe mu da murna. 18Washegari Bulus da sauranmu muka tafi domin mu ga Yaƙub, dukan dattawan kuwa suna nan. 19Bulus ya gaishe su ya kuma ba su rahoto dalla-dalla a kan abin da Allah ya yi a cikin Alʼummai ta wurin aikinsa.

20Da suka ji haka, sai suka yabi Allah. Saʼan nan suka ce wa Bulus: “Ka gani ɗanʼuwa, yawan dubban Yahudawan da suka gaskata, kuma dukansu masu himma ne a wajen bin doka. 21An sanar da su cewa kana koya wa dukan Yahudawan da suke zama a cikin Alʼummai cewa su juye daga Musa, kana kuma faɗa musu kada su yi wa ʼyaʼyansu kaciya ko su yi rayuwa bisa ga alʼadunmu. 22To, me za mu yi ke nan? Lalle za su ji cewa ka iso, 23saboda haka, ka yi abin da muka faɗa maka. Akwai mutum huɗu tare da mu da suka yi alkawari. 24Ka ɗauki waɗannan mutane, ka tafi da su ku tsarkaka gaba ɗaya, ka kuma biya musu kome don su samu su yi aski. Ta haka kowa zai sani babu gaskiya a waɗannan rahotanni game da kai, za a kuma ga cewa kai kanka kana kiyaye dokar. 25Game da Alʼummai masu bi kuwa, mun yi musu wasiƙa a kan shawararmu cewa su guji abincin da aka miƙa wa gumaka, da jini, da naman dabbar da aka maƙure da kuma fasikanci.”

26Washegari, sai Bulus ya ɗauki mutanen ya kuma tsarkake kansa tare da su. Saʼan nan ya tafi haikali domin yǎ sanar da ranar cikar tsarkakewarsu da kuma ranar da za a ba da sadaka domin kowannensu.

An Kama Bulus

27Da kwana bakwai ɗin suka yi kusan cika, waɗansu Yahudawa daga lardin Asiya suka ga Bulus a haikali. Sai suka zuga taron duka, suka kama shi, 28suna ihu suna cewa “Mutanen Israʼila ku taimake mu! Ga mutumin da yake koya wa dukan mutane koʼina cewa su ƙi mutanenmu da dokarmu da kuma wannan wuri. Ban da haka ma, ya kawo Helenawa a cikin filin haikali ya ƙazantar da wurin nan mai tsarki.” 29(Dā ma can sun ga Turofimus mutumin Afisa a birni tare da Bulus suka yi tsammani Bulus ya kawo shi filin haikali.)

30Duk birnin ya ruɗe, mutane suka zaburo da gudu daga kowane gefe. Suka kama Bulus, suka ja shi daga haikali, nan da nan aka rurrufe ƙofofi. 31Yayinda suke ƙoƙari su kashe shi, sai labari ya kai ga shugaban ƙungiyar sojan Roma cewa birnin Urushalima duk ta hargitse. 32Nan da nan ya ɗibi waɗansu hafsoshi da sojoji suka gangara a guje wurin taron. Da masu hargitsin suka ga shugaban ƙungiyar sojan da sojojinsa, sai suka daina dūkan Bulus.

33Shugaban ƙungiyar sojan ya zo ya kama shi ya ba da umarni a ɗaure shi da sarƙoƙi biyu. Saʼan nan ya yi tambaya ko shi wane ne, da kuma abin da ya yi. 34Waɗansu daga cikin taron suka ɗau kururuwa suna ce abu kaza, waɗansu kuma suna ce abu kaza, da yake shugaban ƙungiyar sojan ya kāsa samun ainihin tushen maganar saboda yawan hayaniyar, sai ya yi umarni a kai Bulus barikin soja. 35Saʼad da Bulus ya kai bakin matakala, sai da sojoji suka ɗaga shi sama saboda tsananin haukan taron. 36Taron da suka bi suka dinga kururuwa, suna cewa, “A yi da shi!”

Bulus Ya Yi wa Taron Jawabi

37Da sojoji suka kai gab da shigar da Bulus cikin bariki, sai ya ce wa shugaban ƙungiyar sojan, “Ko ka yarda in yi magana da kai?”

Sai ya amsa, ya ce, “Ka iya Helenanci ne?
38Ba kai ba ne mutumin Masar nan da ya haddasa tawaye har ya yi jagorar ʼyan taʼada dubu huɗu zuwa hamada a shekarun baya?”

39Bulus ya amsa, ya ce, “Ni Bayahude ne, daga Tarsus a Silisiya shahararren birnin nan. In ka yarda bari in yi wa mutane magana.”

40Da ya sami izini daga shugaban ƙungiyar sojan, sai Bulus ya tsaya a matakala, ya ɗaga wa taron hannu. Da dukan suka yi shiru, sai ya ce musu da Aramayanci
Ko kuwa mai yiwuwa Da Ibraniyanci; haka ma a Mat 22.2
:

Copyright information for HauSRK